An tabbatar da Samson Adamu a matsayin Babban Sakatare na dindindin na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), sakamakon kokarin da ya yi a lokacin ya rike kujeran a baya a matsayin na rikon kwarya.
Adamu ya gaji kujeran ne daga hannun Véron Mosengo-Omba, wanda a halin yanzu ya karɓi mukamin Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DR Congo).
Wannan nadi nasa ya sanya shi a shugabancin Sakatariyar CAF, inda zai kula da harkokin gudanarwa na hukumar.
-
Gasar Cin Kofin Duniya ta U15: Najeriya ta doke New Caledonia da Ci 7-0
-
Kano Pillars Para-Soccer za ta fara Gasar World Polio Day a Abuja
-
Lagos za ta karɓi bakuncin bikin bayar da kyaututtukan CAF na 2026
Adamu, sananne ne sosai a fagen gudanarwa na kwallon kafa ta Afirka, inda ya yi aiki a matsayi daban-daban a cikin Hukumar CAF kafin a tabbatar da shi a matsayin Babban Sakatare.
Har wa yau, Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta bakin Babban Sakatarenta, Dr Emmanuel Ikpeme, ta taya Mista Samson Adamu murna bisa tabbatar da shi a matsayin Babban Sakatare na dindindin na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF).
