Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Para-Soccer za ta fara fafatawa a gasar World Polio Day Para-Soccer Tournament ta shekarar 2026, karo na takwas, da ake gudanarwa a Abuja, inda za ta kara da takwararta ta Yobe a yau Laraba, 21 ga Oktoba.

Gasar ta fara ne a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, kuma za a ƙare ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026.

Ƙungiyoyi takwas ne ke fafatawa, waɗanda suka haɗa da Kano, Yobe, Sokoto, Kebbi, Nasarawa, Abuja, Team Founder da Team President.

A cewar sanarwar da jami’in yaɗa labarai na Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ashiru Rabiu Gidan Tudu, ya fitar, an raba ƙungiyoyin zuwa rukuni biyu.

Rukuni na A ya ƙunshi Kano, Yobe, Sokoto da Team President, yayin da Rukuni na B ya haɗa da Abuja, Kebbi, Nasarawa da Team Founder.

Kano Pillars Para-Soccer za ta fuskanci Yobe a wasanta na farko, da fatan samun sakamako mai kyau da zai taimaka mata wajen ci gaba da neman lashe gasar ta bana.

Mai horar da ƙungiyar, Ibrahim Musa, ya ce ’yan wasansa sun kammala shirye-shirye kuma a shirye suke su taka rawar gani.

Ya kuma yaba wa gwamnatin Jihar Kano da shugaban hukumar wasanni, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, bisa goyon bayan da suke bai wa harkokin wasanni a jihar.

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *