Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kafa kwamitin fasaha da zai hanzarta aiwatar da shirye-shiryen bunƙasa kiwo da noman alkama da sauran muhimman kayan abinci a faɗin Najeriya.
Shettima ya bayyana hakan ne bayan ya jagoranci wani babban taro kan yadda harkar noma ke tafiya da matakan da za a ɗauka domin inganta ta.
- Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Ebola a Abuja
- Gwamnatin Tinubu na gina gidaje sama da 10,000 a jihohi 14 da Abuja
Ya ce aikin kwamitin shi ne hanzarta aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara domin ƙara yawan noman alkama da sauran kayan abinci, tare da bunƙasa kiwo a ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci mambobin kwamitin su haɗa ƙwarewa da ra’ayoyinsu domin tsara cikakken tsarin aiwatar da waɗannan shirye-shirye a fannin noma.
Ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakan da za su ƙarfafa samar da abinci da bunƙasa harkar kiwo a Najeriya.