Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce shirin samar da gidaje na Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da gidaje sama da 10,000 da ake ginawa a jihohi 14 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Idris ya ce shirin na da nufin faɗaɗa damar ’yan Najeriya na mallakar gidaje masu araha, inganta rayuwarsu da kuma bunƙasa ayyukan gine-gine a ƙasar.
Ministan ya bayyana hakan ne a bikin cika shekaru 20 da kafuwar Kamfanin Raya Gidaje na Abuja (APDC), inda aka gudanar da liyafar bayar da kyaututtuka.
- ’Yan sanda sun kama mutane 11 da ake zargi da fashi da makami da damfarar fasinjoji a Abuja
- ADC ta ce kalaman Yari sun nuna gazawar APC wajen magance matsalar tsaro
Ya ce ya taɓa zama shugaban kwamitin gudanarwa na kamfanin a wa’adi biyu, tare da bayyana godiyarsa bisa kyautar da kamfanin ya ba shi domin girmama gudummawar da ya bayar a lokacin aikinsa.
Idris ya yi fatan kamfanin APDC zai yi amfani da gogewar da ya samu cikin shekaru 20 wajen ci gaba da taimakawa wajen raya Abuja ta hanyar samar da gidaje masu inganci da gudanar da ayyukan gine-gine cikin gaskiya da kulawa.