Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC ta gudanar da taronta na farko, inda ta yanke muhimman shawarwarin da za su taimaka wajen cimma nasarar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Uzodimma, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mambobin majalisar sun nuna himma da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora musu.
- ’Yan sanda sun kama waɗanda ake zargi da fashi, kisan kai da safarar miyagun ƙwayoyi a Bauchi
- Shettima ya kafa kwamitin bunkasa kiwo da noman kayan abinci a Najeriya
Ya ce ƙudurin mambobin zai ƙara ƙarfi ne sakamakon jajircewar Tinubu wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen jam’iyyar da ke da nufin inganta rayuwar ’yan Najeriya.
Gwamnan ya bayyana cewa majalisar za ta ci gaba da wannan ƙoƙari domin ƙarfafa nasarorin da ta samu da kuma tabbatar da cewa al’umma sun amfana da manufofin gwamnatin APC.
Ya jaddada cewa babban burin majalisar shi ne gudanar da ayyukan da za su taimaka wa Tinubu wajen samun nasara a zaɓe mai zuwa.