Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ƙaddamar da sabuwar gadar masu tafiya a ƙasa da ke kan babbar hanyar Airport Expressway mai layuka goma, wadda cocin Dunamis International Gospel Centre ta gina a kusa da cibiyarta ta Glory Dome da ke Abuja.

A wajen bikin ƙaddamar da gadar ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026, Wike ya yaba wa babban faston cocin, Paul Enenche, da matarsa Becky, bisa gina gadar domin kare rayukan masu tafiya a ƙasa.

Ya ce irin wannan gudummawa daga ƙungiyoyi masu zaman kansu na taimaka wa gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa.

Ministan ya kuma sanar da cewa gwamnatin Abuja za ta biya kashi 50 cikin 100 na kuɗin da aka kashe wajen gina gadar.

Ya umarci babban sakataren hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA), Richard Yunana Dauda, da ya tattauna da shugabannin cocin domin tantance kuɗin aikin da kuma kammala shirin mayar musu da kuɗin.

Wike ya ce cocin ta fara neman izinin gina gadar tun a shekarar 2018, amma an sake duba buƙatar tare da bayar da izini a cikin wata guda bayan an gabatar masa da ita a watan Fabrairun 2026.

Ya kuma bukaci mazauna Abuja da matafiya su riƙa amfani da gadar maimakon tsallaka babbar hanyar da ke da saurin ababen hawa.

Ministan ya kuma yi kira ga al’ummar Najeriya da su zaɓi shugabannin da ke da ƙwarewar jagoranci, yana mai cewa wasu daga cikin sukar da ake yi wa gwamnati a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce ke haddasa su.

A nasa jawabin, fasto Paul Enenche ya ce cocin ta gina gadar ne domin nuna ƙauna da hidima ga al’umma, yayin da kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) a Abuja, Tijani Ilyasu, ya ce gadar za ta taimaka wajen rage haɗurran masu tafiya a ƙasa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *