Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya umarci Hukumar Kare Bayanai ta Ƙasa (NDPC) da ta gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin amfani da hotunan da aka ƙirƙira da fasahar AI da kuma sauya bayanan wasu mutane a rajistar masu zaɓe ta INEC.
kungiyar ta bai wa gwamnatin wa’adin kwana bakwai domin ɗaukar matakan da ta nema.
A cikin wasiƙar da ta aika wa Tinubu a ranar 31 ga Oktoba, 2026, SERAP ta buƙaci kwamishinan NDPC, Dakta Vincent Olatunji, ya binciki yadda aka samu bayanan da ake zargi da kura-kurai, adadinsu da wuraren da abin ya shafa, tare da gano waɗanda ke da hannu.
- An tabbatar da babu Ebola a mutane biyu da ake zargi a Adamawa
- Lalong ya taya tsohon gwamnan Filato Ambasada Tapgun murnar cika shekara 85
Ƙungiyar ta kuma nemi NDPC ta gudanar da binciken na’ura mai zurfi kan bayanan da tsarin kwamfutocin INEC, domin tantance ko an samu kutse ko sauya bayanan sirrin ’yan Najeriya ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ko an karya dokar kare bayanai ta shekarar 2023.
SERAP ta ce INEC ta riga ta amince da samun hotunan da ake zargin na AI ne da wasu bayanan rajista masu matsala, yayin baje kolin rajistar daga 9 zuwa 15 ga Oktoba.
Hukumar zaɓen ta ce tana gudanar da tantancewa da gyara bayanan kafin tabbatar da cikakkiyar rajistar masu zaɓe a ranar 15 ga Disamba, 2026.
Ƙungiyar ta ce idan ba a ɗauki matakan da ta nema cikin kwana bakwai ba, za ta yi la’akari da ɗaukar matakin shari’a.
Ta kuma jaddada cewa ya kamata a bai wa waɗanda bayanansu suka samu matsala damar tantancewa da gyara su, ba tare da an hana su damar shiga zaɓen 2027 bisa kuskure ba.