Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce sababbin dakarunta 816 sun kammala atisayen kwanaki shida na gwajin ƙarfin jiki da dabarun yaƙi a sansaninta da ke Kaduna.
Atisayen mai suna Exercise MUN FARA ya gudana daga ranar 12 zuwa 17 ga Oktoba, 2026, inda aka gwada ƙwarewar sojojin wajen zirga-zirga da rana da dare, sintiri, kwanton ɓauna, kai hare-hare da kafa tantuna a cikin daji.
Atisayen ya ƙare da gasar gudu mai nisan kilomita 20, inda rundunar Alpha-Jet ta zo ta farko cikin sa’o’i biyu da mintuna 33 da daƙiƙu bakwai.
- An tabbatar da babu Ebola a mutane biyu da ake zargi a Adamawa
- SERAP ta bai wa Tinubu wa’adin kwana bakwai a bincike kura-kuran rajistar masu zaɓe
Soja Mohammed U na rundunar MI-35 ya zo na farko a rukunin maza, yayin da Salihu SO na rundunar ATR-42 ya jagoranci rukunin mata.
Kwamandan cibiyar horas da sojojin, Air Commodore AO Akins, ya yaba wa dakarun kan juriyarsu, ladabinsu da haɗin kansu, yana mai cewa atisayen ya gwada yadda suke amfani da dabarun aikin soja, sarrafa makamai da karanta taswira.
Ya ce atisayen wani ɓangare ne na shirin horas da sojojin domin ƙarfafa ƙwarewarsu da shirya su tunkarar ayyukan soja, kafin su kammala atisayen ƙarshe na cikin daji da fara aiki a rundunar sojin saman Najeriya.