Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ba ya kallon rashin nasarar ’yan jam’iyyar Republican a zaɓukan da aka gudanar a matsayin kayen da ya sha da kansa, yana mai cewa shi bai tsaya takara a zaɓukan ba.

Trump ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan ra’ayin cewa sakamakon zaɓukan ya nuna an kayar da shi a siyasance.

Ya ce: “Ba na son kallon hakan a matsayin shan kaye. A ganina, ni ban tsaya takara ba.”

Sai dai Trump ya bayyana takaicinsa kan ’yan Republican da suka sha kaye, yana mai cewa yana tausaya wa da dama daga cikinsu, waɗanda ya bayyana a matsayin mutanen kirki da masu kishin ƙasa.

Ya kuma yi tsokaci kan fafatawar siyasa da ya shafe shekaru yana yi da ’yan Democrat, yana mai bayyana dalilin da ya sa ba ya ɗaukar sakamakon zaɓukan na wannan dare a matsayin rashin nasara ta kansa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *