Trump ya bayyana hakan ne lokacin da yake mayar da martani kan ra’ayin cewa sakamakon zaɓukan ya nuna an kayar da shi a siyasance.
- Tambuwal ya zargi gwamnatin Sakkwato da tauye ’yancin siyasar ’yan adawa
- Sarkin Musulmi ya karrama shugaban JIBWIS da lambar yabo kan hidimar ilimi da addini
Ya ce: “Ba na son kallon hakan a matsayin shan kaye. A ganina, ni ban tsaya takara ba.”
Sai dai Trump ya bayyana takaicinsa kan ’yan Republican da suka sha kaye, yana mai cewa yana tausaya wa da dama daga cikinsu, waɗanda ya bayyana a matsayin mutanen kirki da masu kishin ƙasa.
Ya kuma yi tsokaci kan fafatawar siyasa da ya shafe shekaru yana yi da ’yan Democrat, yana mai bayyana dalilin da ya sa ba ya ɗaukar sakamakon zaɓukan na wannan dare a matsayin rashin nasara ta kansa.