Dan takarar jam’iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Amurka a Jihar Michigan, inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican, Mike Rogers.

Nasarar ta sa El-Sayed ya kafa tarihi a siyasar Amurka, inda ya zama Musulmi na farko da aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan ƙasar.

Haka kuma, sakamakon zaɓen ya taimaka wa jam’iyyar Democrat wajen ci gaba da riƙe kujerar Sanatan da take da ita a Jihar Michigan.

Wannan nasara ta zo ne a zaɓukan da aka gudanar a Amurka, inda jam’iyyun Republican da Democrat suka fafata a neman muƙamai daban-daban.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *