Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA), reshen Jihar Kano, ta taya Air Commodore Salisu Yusha’u (mai ritaya) murnar naɗa shi kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya naɗa Salisu Yusha’u a matsayin kwamishinan a ranar 30 ga Oktoba, 2026.

A cikin saƙon taya murnar, kwamandan NDLEA na Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal, ya bayyana sabon kwamishinan a matsayin ƙwararren jami’in tsaro da ya shahara wajen jajircewa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.

Lawal ya ce yana da yakinin cewa sabon kwamishinan zai yi amfani da ƙwarewa da gogewar da ya samu a tsawon aikinsa a rundunar sojin saman Najeriya, inda ya kai matsayin Air Commodore, wajen yi wa al’ummar Jihar Kano hidima.

Ya kuma yi masa addu’ar samun nasara a sabon muƙaminsa, tare da bayyana fatan ƙarfafa haɗin gwiwar da ke tsakanin gwamnatin Kano da NDLEA wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu a jihar.

Saƙon, wanda jami’in hulɗa da labarai na NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, ya jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwar hukumomin wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *