Hakeem Baba-Ahmed, shugaban jam’iyyar SDP, ya ce sakamakon zaɓukan da aka gudanar a Amurka ya nuna illar da shugabanni ke fuskanta idan suka yi watsi da halin da al’umma ke ciki.

Ya ce da a ce shugabannin Najeriya sun ba da damar gudanar da sahihin zaɓe, da sun ga irin yadda al’umma za su iya bayyana matsayarsu ta hanyar ƙuri’a.

A cikin saƙon nasa, Baba-Ahmed ya zargi shugabannin Najeriya da mayar da talakawa mabarata, ta hanyar barin su cikin mawuyacin hali, sannan su riƙa ba su tallafi ko abin da ya kira tsaba bayan sun sha wahala.

Ya ƙara da cewa al’umma na ci gaba da jiran ranar zaɓe domin su bayyana matsayarsu, yana mai addu’ar Allah Ya kai su wannan rana.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *