Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 18 Brigade sun ceto mutum 16 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Neja, tare da ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu, bama-baman RPG uku da babura 33.

Sojojin sun gudanar da aikin ne a ranar 5 ga Nuwamba, 2026, bayan samun bayanan sirri kan motsin ’yan bindiga daga ƙaramar hukumar Mashegu zuwa Rijiyan Nagwamatse da ke ƙaramar hukumar Kontagora ta Jihar Neja.

Sanarwar da mukaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin ta 18 Brigade, Kyaftin Adebayo Samuel Adewumi, ya fitar ranar Juma’a, ta ce sojojin sun yi wa ’yan bindigar kwanton ɓauna a kan hanyar da ake zargin za su bi, inda suka yi musayar wuta tare da kashe wasu daga cikinsu waɗanda ba a tantance adadinsu ba, sannan suka kuɓutar da mutanen 16.

Baya ga bindigogin AK-47 guda biyu, sojojin sun ƙwato harsasai, bama-baman RPG masu fashewa guda uku, babura 33 da kuɗi Naira miliyan 4 da dubu 105.

A wani samamen daban da aka gudanar ranar 3 ga Nuwamba, sojojin sun kuma tare wasu ’yan bindiga da ke kan hanyarsu daga Jihar Kebbi zuwa ƙaramar hukumar Rijau ta Jihar Neja, inda suka tilasta musu tserewa zuwa cikin daji bayan musayar wuta.

Binciken da sojojin suka gudanar a yankin ya kai ga ƙwato babura biyar, wayar salula da kuɗi Naira dubu 644 da ɗari 300, tare da wasu kayayyaki.

An ba mutanen da aka ceto agajin gaggawa kafin miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa domin haɗa su da iyalansu.

Kwamandan rundunar 18 Brigade ya yaba wa dakarun bisa jajircewarsu, tare da umartar su da ci gaba da ƙoƙarin kawar da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a yankin da ke ƙarƙashin rundunarsa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *