Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta ce ta kama mutum 26 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da daba, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, safarar tabar wiwi, satar wayoyin lantarki da kuma yunƙurin yin tsafin kuɗi a jihar.
Kakakin rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa an kama mutum bakwai a yankunan Albishir da Gurara da ke Minna, bisa zargin hannu a hare-haren daba da raunata mutane.
Binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga ramuwar gayya kan wani artabu da ya faru a wani biki a Albishir a shekarar 2025, wanda ya yi sanadin mutuwar wani Sani Mohammed na Gurara.
Ya ce a wani rikici daban da ya faru tsakanin matasan Kafintela da Samande a ranar 16 ga Oktoba, an kama mutum 11, yayin da wasu mutum 13 kuma aka kama a rikicin matasa tsakanin Angwan-Biri da Tudun-Fulani da ke ƙaramar hukumar Bosso.
- Idris ya buƙaci kwamishinonin APC su yaƙi bayanan ƙarya, su saurari koke-koken jama’a
- Sojoji sun ceto mutum 16 da aka yi garkuwa da su, sun ƙwato bindigogi da babura 33 a Neja
Rundunar ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.
A wani samame kuma, ’yan sanda sun kama mutum biyar a Garima da ke Bosso bisa zargin yunƙurin yin tsafin kuɗi ta amfani da ƙasusuwan mutum da kuma cutar da dabbobin gida.
Rundunar ta ce ta ƙwato kayan da ake zargin an yi amfani da su wajen gudanar da tsafin, ciki har da tufafi masu jini, ƙwaryoyi huɗu, kaji da wuka mai jini.
Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum bakwai bisa zargin satar wayoyin lantarki da lalata tiransifoma a Minna da Lambata, tare da ƙwato kayan aiki da wayoyin lantarki da aka cire.
A wani lamari daban, ta kama wani Adamu Abubakar da ake zargi da hannu a yunƙurin satar awaki a Maitumbi, yayin da direbansa mai suna Danlami ya tsere kuma ake nemansa.
Sanarwar da kakakin rundunar ya fitar ranar 5 ga Nuwamba, 2026, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan wasu daga cikin waɗanda aka kama, yayin da aka gurfanar da wasu a kotu. Rundunar ta kuma ce za ta ci gaba da sintiri da sa ido domin tabbatar da tsaro a sassan jihar.