Rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) ta ce ta gano na’urar nadar muryar matuƙan jirgin (Cockpit Voice Recorder) na jirgin ATR-42 da ya yi haɗari a Igbokoda da ke Jihar Ondo, yayin da ake ci gaba da aikin bincike da kwato sauran kayayyakin jirgin.
Rundunar ta ce ƙwararrun jami’anta tare da na Hukumar Binciken Haɗurra ta Najeriya (NSIB) sun tabbatar da cewa na’urar tana nan ba tare da ta lalace ba.
Haka kuma, an gano wani ɓangare na na’urar adana bayanan zirga-zirgar jirgin (Flight Data Recorder), wadda aka fi sani da Black Box, yayin da ake ci gaba da neman sauran ɓangaren.
- Peter Obi ya tattauna da tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya kan zaɓe da tsadar rayuwa
- APC ta zargi ADC da sukar kotu idan hukunci bai yi mata daidai ba
Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa an kuma gano wasu tarkacen jirgin, sassan injinsa da gawarwakin wasu mutane.
Ya ce ana ci gaba da aikin a cikin dajin fadama mai wahalar shiga, domin kwato sauran sassan jirgin da gudanar da binciken fasaha.
Ya ƙara da cewa ana gudanar da binciken cikin taka-tsantsan, bisa hujjoji, domin gano cikakken abin da ya haddasa haɗarin.
Rundunar ta ce ana kuma kula da yadda ake tattara gawarwakin da aka gano da kuma tantance su, tare da ci gaba da tuntubar iyalan waɗanda abin ya shafa domin ba su bayanai da tallafi.
Haka kuma, tana tattaunawa da hukumomin da abin ya shafa kan matsalolin muhalli da al’ummar yankin suka gabatar.