Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya karɓi baƙuncin wata tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a cibiyar Obidient House da ke Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi Najeriya.

Obi ya ce taron ya gudana ne a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, kwana guda bayan ganawarsa da wakilan Hukumar Tarayyar Turai (EU).

Ya bayyana cewa sun tattauna matsalar tsadar rayuwa, jin daɗin al’umma da kuma sahihancin zaɓe mai zuwa.

Ya ce ya yi amfani da damar wajen kira ga ƙasashen duniya da su mara wa ’yan Najeriya baya wajen kare ’yancinsu na zaɓar shugabanninsu cikin lumana, ta hanyar zaɓe na gaskiya, adalci da sahihanci.

Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya ta kasance ƙarƙashin jagorancin Leonardo Santos Simão, tsohon Ministan Harkokin Wajen Mozambique, wanda a yanzu shi ne Wakili nA Musamman na Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka ta Yamma.

Obi ya gode wa Simão da sauran mambobin tawagar bisa ziyarar da tattaunawar da suka yi, yana mai jaddada cewa har yanzu yana ganin yiwuwar samar da sabuwar Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *