Jam’iyyar APC mai mulki ta buƙaci jam’iyyar ADC da ta warware rikicin shugabancinta, maimakon ɗora wa gwamnatin tarayya da ɓangaren shari’a alhakin hukuncin kotu na baya-bayan nan.

Sakataren Yaɗa Labaran APC na Ƙasa, Felix Morka, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce jam’iyyarsa ba ta da hannu a takaddamar shari’ar da ta kai ga cire shugabancin ADC ƙarƙashin jagorancin David Mark da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi.

Morka ya ce rikicin ya samo asali ne daga ƙarar da wasu jami’an ADC na ƙasa suka shigar, inda suka zargi David Mark da abokan tafiyarsa da karɓe ikon jam’iyyar ba tare da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyyar cikin gida da doka ba.

Ya bayyana hukuncin kotun a matsayin shaida ta ’yancin kai na ɓangaren shari’a, tare da kira ga ADC da ta ɗaukaka ƙara idan ba ta gamsu da hukuncin ba.

Haka kuma, kakakin APC ya zargi ADC da nuna zaɓaɓɓen yadda take mutunta hukuncin kotu, inda ya ce jam’iyyar na yabon ɓangaren shari’a idan hukunci ya yi mata daidai, amma ta soki shi idan hukuncin bai dace da muradunta ba.

Morka ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na nan kan aniyarta ta kare bin doka da oda, hukumomin dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawan shugabanci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *