Mataimakin Daraktan Cibiyar Kukah (TKC), Dakta Emmanuel Nkanta, ya jagoranci tawagar Wakilai ta Musamman na Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a Afirka ta Yamma da yankin Sahel, Leonardo Santos Simão, zuwa ganawa da Shugaban Kwamitin Samar da Zaman Lafiya na Ƙasa (NPC), Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.
Ziyarar na cikin jerin shawarwarin da Simão ke yi da shugabannin siyasa, hukumomin zaɓe da sauran masu ruwa da tsaki a yankin, domin tattauna shirye-shiryen zaɓen Najeriya na shekarar 2027.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan yanayin siyasa da zaɓe a ƙasar, ƙalubalen da ake fuskanta da kuma hanyoyin haɗin gwiwa wajen tabbatar da zaɓe cikin lumana, gaskiya da bai wa kowa dama.
- Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su karɓi katin zaɓensu
- Atiku ya ce babu hukuncin kotu da zai hana shi tsayawa takara a 2027
A yayin ganawar, Abdulsalami ya yi wa tawagar bayani kan shirye-shiryen kwamitin da tattaunawar da yake yi da masu ruwa da tsaki.
Ya kuma jaddada muhimmancin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasa karo na biyu, inda ya buƙaci jam’iyyu da ’yan takara su guji tashin hankali, su kuma bi hanyoyin shari’a idan aka samu saɓani kan sakamakon zaɓe.
A nasa ɓangaren, Simão ya sake tabbatar da aniyar Majalisar Ɗinkin Duniya na tallafa wa kwamitin da ƙarfafa hukumomin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ya kuma bayyana fatan cewa za a yi amfani da darussan zaɓukan baya wajen inganta gaskiya, sahihanci da zaman lafiyar zaɓen 2027.