Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce yana nan a cikin masu neman shugabancin Najeriya, kuma babu wani hukuncin kotu da zai sa ya janye daga takararsa ko ya hana shi kasancewa a kan takardar zaɓe.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 6 ga Nuwamba, 2026, inda ya ce bai kamata a ɗauki hukuncin kotu na baya-bayan nan a matsayin ra’ayin al’ummar Najeriya ba.
Ya kuma jaddada cewa dole ne a bai wa ’yan ƙasa damar zaɓar shugabannin da suke so.
Atiku ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da matsin lambar siyasa, ƙirƙirar labaran ƙarya da kuma wasu matakan shari’a wajen raunana jam’iyyun adawa.
- WHO: Matakan yaƙi da sauyin yanayi shida za su iya ceton rayuka miliyan 1.6 duk shekara
- INEC ta musanta sake tabbatar da shugabancin David Mark a ADC
Ya kuma yi zargin cewa ana ƙoƙarin yin maguɗi a rajistar masu zaɓe ta hanyar amfani da hotunan da aka ƙirƙira da fasahar AI, sunayen ƙarya da kuma mutanen da babu.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya soki matakan tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai danganta cire tallafin man fetur, faɗuwar darajar Naira da tsadar abinci da wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ya kuma ambaci rufe masana’antu da ƙananan sana’o’i, ƙaura da matasa ke yi da kuma matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar.
Atiku ya ce zai ci gaba da yaƙin neman zaɓensa, yana mai cewa ba zai bari barazana ko wani matakin shari’a ya hana shi shiga takara ba.
Ya kuma bayyana cewa Najeriya na buƙatar tsarin dimokuraɗiyya da zai bai wa jam’iyyu da ra’ayoyi daban-daban damar fafatawa, inda ya ce ya kamata a bar ’yan Najeriya su yanke hukunci ta hanyar zaɓe.