Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana wani saƙo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa ta sake tabbatar da shugabancin Sanata David Mark a jam’iyyar ADC, a matsayin ƙarya.
Hukumar ta ce ba ita ta fitar da hoton sanarwar da saƙon da ke tare da shi ba, inda ta ƙara da cewa ba ta amince da amfani da tambarinta da hoton Kwamishinanta na Ƙasa, Mohammed Haruna, a cikin sanarwar ba.
- ’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin satar sandunan fitilun tituna a Abuja
- UNICEF: Hare-hare kan hanyoyin samar da ruwa a wuraren yaƙi na ƙara jefa yara cikin haɗari
INEC ta jaddada cewa ba ta fitar da wata sanarwa da ke sake tabbatar da shugabancin David Mark a jam’iyyar ADC ba.
Saboda haka, hukumar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da wannan saƙo gaba ɗaya, tare da bin sahihan bayanai daga shafukanta na hukuma da aka tantance.