Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Warri, Jihar Delta, ta yanke wa wasu mutane 10 hukuncin daurin shekaru biyu zuwa uku a gidan yari bisa samunsu da laifin safarar man fetur ba bisa ka’ida ba.
Mai shari’a H.A. Nganjiwa ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan waɗanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa.
Hukumar EFCC shiyyar Benin ce ta gurfanar da su bisa zargin haɗa baki da safarar man fetur ba bisa ƙa’ida ba.
- UNICEF: Hare-hare kan hanyoyin samar da ruwa a wuraren yaƙi na ƙara jefa yara cikin haɗari
- WHO: Matakan yaƙi da sauyin yanayi shida za su iya ceton rayuka miliyan 1.6 duk shekara
Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da James Terry, Gift Ezewu Godfrey, Obidi Peter Obi, Anthony Onyebuchi Edekobi da Victor Ataria Sule. Sauran sun kasance Jubril Abubakar, Auwal Aliyu, Nnaemeka Nwobodo, Victor Edem da Sunday Ndem Eyere.
Kotun ta yanke wa James Terry da Gift Ezewu Godfrey hukuncin daurin shekaru biyu ko biyan tarar Naira 300,000 kowannensu.
Sauran takwas kuma sun samu hukuncin daurin shekaru uku, inda aka ci tarar Naira 300,000 ga shida daga cikinsu, Naira 350,000 ga Anthony Onyebuchi Edekobi da Naira 400,000 ga Sunday Ndem Eyere.
Rahoton EFCC ya ce an fara cafke mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro game da wasu ayyukan da ake zargin suna yi a Koko, ƙaramar hukumar Warri ta Arewa a Jihar Delta.
Bincike ya danganta su da safarar man dizal (AGO) wanda bai kai ƙa’idar ingancin da ake buƙata ba.