A wani sabon rahoto da hukumar ta fitar ranar 4 ga Nuwamba, 2026, WHO ta bayyana cewa aiwatar da matakan a faɗin duniya na iya samar da ribar tattalin arziki ta dala tiriliyan 3.9 a duk shekara, tare da ƙarin ribar kuɗaɗen shiga na gwamnati da ta kai dala tiriliyan 5.4.
Matakan sun haɗa da samar da tsarin gargaɗin jama’a kan illolin tsananin zafi, inganta hanyoyin samar da ruwan sha da tsaftar muhalli, samar da wuraren wanke hannu, amfani da makamashi mai tsafta wajen girki da dumama gidaje, da kuma inganta tsarin haraji kan man fetur domin rage amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli.
- ’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin satar sandunan fitilun tituna a Abuja
- ’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin satar sandunan fitilun tituna a Abuja
Daraktan WHO, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce rikicin sauyin yanayi rikicin lafiya ne, amma ana iya hana yawancin illolinsa ta hanyar amfani da hanyoyin da ake da su a yanzu.
Ya ce rahoton ya nuna cewa matakan da suka dace za su iya ceton miliyoyin rayuka, musamman a ƙasashen da suka fi buƙatar taimako.
Rahoton ya kuma kiyasta cewa matakan za su taimaka wajen rage hayakin Carbon Dioxide (CO₂) da ya kai tan biliyan 16.7, kwatankwacin kashi 31 cikin 100 na hayakin da duniya ke fitarwa duk shekara, ban da wanda ke da alaƙa da amfani da filaye da sauye-sauyen su.
WHO ta kuma ce duk dala ɗaya da aka zuba a cikin biyar daga cikin matakan za ta iya samar da ribar dala 24, yayin da tsarin gargaɗin tsananin zafi zai iya samar da ribar dala 835 kan kowace dala ɗaya da aka kashe.