Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kuɗi na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Fifth Committee), kuma Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar, Sanata Jimoh Ibrahim, ya yi gargaɗi kan ƙarin kuɗaɗen da ba a tsara ba, jinkirin kammala ayyuka da kuma rashin cimma manufofin da aka sa gaba a ayyukan gine-ginen Majalisar na shekarar 2027.

Jimoh Ibrahim ya jaddada cewa dole ne a kammala dukkan ayyukan cikin kasafin kuɗin da aka amince da shi, tare da bin wa’adin da aka tsara da kuma cimma manufofin da aka tanada domin inganta rayuwar al’ummomi a sassan duniya.

Ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin ya sake fara tattaunawa kan kasafin kuɗin Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2027.

A yayin zaman, kwamitin ya kuma duba halin da kuɗaɗen ƙungiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya suke ciki, da kuma shirin Capital Master Plan, tare da sake jaddada muhimmancin kula da kasafin kuɗi cikin gaskiya da riƙon amana.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *