Tawagar D’Tigress ta Najeriya

Tawagar D’Tigress ta Najeriya ta sha kaye na biyu a jere a Gasar Cin Kofin Ƙwallon Kwando na Duniya ta 2026, inda Hungary ta doke ta da ci 71-67 a wasan rukuni na ‘B’ da suka buga a Berlin, a ranar Asabar.

Bayan ta fara gasar da shan kashi da ci 99-81 a hannun Koriya ta Kudu, D’Tigress ta na cikin matsananciyar buƙatar nasara akan Hungary, amma zakaran ta Afirka ta sake fuskantar koma baya yayin da Hungary ta yi nasara akanta.

Wannan shan kashi na tazarar maki 4 abun takaici ne ga Najeriya, wadda ta fafata wasan cikin kuzari da ƙarfin gwiwa amma haƙanta bai cimma ruwa ba.

Wannan sakamako ya bar D’Tigress ba tare da nasara ba a wasanni biyu na farko na Rukunin B, sannan kuma hakan ya jefa damarta ta shiga zagaye na gaba cikin hatsari mai girma.

A halin yanzu, dole Najeriya ta ƙara shiri mai ƙarfi don fuskantar ƙasar Faransa a wasan su na ƙarshe na Rukunin ‘B’, a ranar Litinin.

D’Tigress ta isa Berlin da babban tsammani saboda tarihin da ta ajiye a Gasar Olympics na Paris 2024, inda ta zama tawagar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka ta farko da ta kai matakin kwata fainal.

Kazalika, ta cancanci ta yi abun kirki a Kofin Duniya saboda ita ce zakarar mata ta Gasar AfroBasket.

Amma a maimakon haka, tawagar ta Rena Wakama, tana fafutukar neman rayuwa a Berlin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *