Gwamnatin Jihar Plateau ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar na wani dan lokaci, a matsayin matakin kariya daga wasu da ake zargin sun kamu da cutar diphtheria.
Gwamnatin ta bayar da umarnin ne a ranar Asabar, a cikin wata sanarwa da Kwamishiniyar Yada Labarai, Joyce Ramnap, ta fitar.
A cewar sanarwar, rufe makarantun zai fara ne daga ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, kuma za a ci gaba da rufe su “har sai an ba da wani sabon umarni.”
- Gobara ta kone gidaje shida da shaguna a kasuwar kofar Wanbai Kano
- Soji sun kashe ɗan ta’adda, sun kwato babura huɗu a Katsina
- ‘Yan Boko Haram sun kai hari kan tawagar dan takarar gwamnan APC a Borno
An bayar da umarnin ne karkashin jagorancin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar.
Sanarwar ta ce matakin ya zama dole ne domin daukar matakan kariya daga barkewar cutar diphtheria, bayan samun wasu mutane da ake zargin sun kamu da cutar a wasu sassan jihar, musamman Kananan Hukumomin Jos North da Wase da Jos South da Bassa.
Gwamnatin ta ce umarnin ya shafi dukkan makarantu, ciki har da wadanda suka riga suka fara karatun zangon farko na sabuwar shekarar karatu.
Gwamnatin ta bukaci iyaye da malamai da masu makarantu da su bi umarnin gaba daya.
Jami’an lafiya sun bukaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun kammala dukkan alluran rigakafin da ake ba yara bisa tsarin yau da kullum.
Sun kuma shawarci jama’a da su rika tsaftace hannayensu, sannan su kai yara asibiti ko cibiyar lafiya mafi kusa nan take idan suka fara nuna alamomi kamar zazzabi, ciwon makogwaro ko wahalar numfashi.