Dakarun Rundunar Operation FANSAN YAMMA, sun kashe wani ɗan ta’adda tare da kwato babura huɗu da wasu kayayyaki a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Dan Musa ta jihar Katsina.

Cikin wata sanarwar da ta fito daga Laftanar Kanal Aliyu Danja, Jami’in Yaɗa Labarai na Operation FANSAN YAMMA, ta ce an gudanar da samamen ne a ranar 4 ga Satumba, 2026, bayan dakarun sun samu sahihan bayanan sirri kan kasancewar ‘yan ta’adda a yankin da ke kewaye da dajin Yantumaki.

Bayan samun bayanan, dakarun sun gudanar da wani samame na haɗin gwiwa kan ‘yan ta’addan, inda suka yi musu luguden wuta.

Hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa zuwa cikin dazuzzukan da ke kewaye da yankin.

A yayin binciken yankin bayan samamen, dakarun sun tabbatar da kashe wani ɗan ta’adda guda ɗaya.

Haka kuma, sun kwato babura huɗu da wayar hannu guda da kuma abubuwan ƙarin ruwa wato drip guda biyar da babu komai a cikinsu.

Rundunar ta ce ana zargin an yi amfani da drip ɗin wajen kula da ‘yan ta’addan da suka samu raunuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *