Sabon Shugaban sashen BBC hausa bahaushe

Tun lokacin da Sashen Hausa na BBC ya fara aiki a ranar 13 ga watan Maris 1957, ya zama ɗaya daga cikin fitattun kafafen yaɗa labarai da suka taimaka wajen isar da labarai, ilimi da bayanai ga al’ummar Hausawa a sassan duniya.

A tsawon kusan shekaru 70, sashen ya samu shugabanni daban-daban, ciki har da Hausawa da suka taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda BBC Hausa ke gudanar da aikinta.

Yanzu nadin Haruna Ibrahim Kakangi a matsayin sabon editan sashen ya sake dawo da hankali kan tarihin waɗanda suka gabace shi.

  1. Isa Abba Adamu

Isa Abba Adamu na daga cikin fitattun mutanen da suka jagoranci BBC Hausa.

Ɗan asalin jihar Kano ne, kuma ya shafe shekaru yana aiki da BBC kafin daga bisani ya riƙe manyan mukamai a hukumar.

Shugaban sashen BBC Hausa na farko ba haushe

Adamu ya kuma shiga tarihi a matsayin ɗaya daga cikin manyan ’yan Najeriya da suka taka rawa wajen tsarawa da bunƙasa aikin BBC Hausa, musamman wajen haɓaka amfani da Hausa wajen bayyana sabbin kalmomi da dabarun sadarwa.

Daga baya ya zama Executive Editor na BBC Africa, kafin rasuwarsa a shekarar 2021.

  1. Jamilah Tangaza

Jamilah Tangaza ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mata da suka jagoranci Sashen Hausa.

Ta shiga BBC a shekarar 1992 a matsayin mai shirya shirye-shirye, kafin ta zama Senior Producer.

Ta kuma taɓa zama Acting Head na BBC Hausa tsakanin 2005 zuwa 2006, sannan daga baya ta zama shugabar sashen.

Shugabar sashen hausa ta biyu bahaushiya

Zamanin Tangaza ya zo ne a lokacin da BBC Hausa ke ƙara faɗaɗa aikinta daga rediyo zuwa intanet da wayoyin hannu, lamarin da ya nuna farkon sauyin sashen zuwa tsarin watsa shirye-shirye na zamani.

  1. Mansur Liman

Sunanan Mansur Liman ya kasance wani muhimmin suna a tarihin jagorancin BBC Hausa.

A lokacin da yake editan sashen, BBC ta ƙara mayar da hankali kan fasahar zamani da kuma yadda masu sauraro ke amfani da wayoyin hannu wajen samun labarai.

shugaban sashen hausa na uku bahaushe

A shekarar 2013, Liman ya gabatar da sabon tsarin shafin BBC Hausa na wayar hannu, wanda aka ƙera domin sauƙaƙa wa masu amfani da wayoyi samun labarai.

Zamaninsa ya kasance wani muhimmin mataki wajen sauya BBC Hausa daga kafar rediyo kawai zuwa kafar yaɗa labarai mai amfani da fasahar dijital.

Jimeh Saleh ya jagoranci BBC Hausa a wani lokaci mai muhimmanci, musamman yayin da sashen ke ƙara faɗaɗa ayyukansa na intanet da sauran kafafen dijital.

A zamaninsa ne aka ƙaddamar da gasar rubutun gajerun labarai ta mata, wadda daga baya ta shahara da suna “Hikayata”.

Manufar gasar ita ce bai wa mata masu rubutu da Hausa damar bayyana basirarsu da labaran da suka shafi rayuwarsu.

Shugaban sashen BBC hausa na hudu bahaushe

Haka kuma, lokacin da BBC Hausa ke bikin cika shekaru 60 a 2017, Saleh ya bayyana buƙatar sashen ya ci gaba da ƙirƙirar sababbin hanyoyin sadarwa da masu sauraro a daidai lokacin da yanayin amfani da kafafen dijital ke sauyawa.

  1. Aliyu Abdullahi Tanko

Aliyu Abdullahi Tanko ya karɓi ragamar editan BBC Hausa a shekarar 2020, inda ya zama ɗaya daga cikin editocin da suka fi daɗewa a wannan mukami.

Shugaban sashen BBC hausa na biyar bahaushe

Zamaninsa ya zo ne a lokacin da aikin BBC Hausa ya ƙara karkata zuwa digital, da bidiyo, da kafofin sada zumunta da sauran hanyoyin da ake amfani da su wajen isa ga masu sauraro.

Tanko ya bar BBC a watan Agustan 2025 bayan ya yi kusan shekaru biyar yana riƙe da mukamin editan sashen.

  1. Haruna Ibrahim Kakangi

Yanzu an ba Haruna Ibrahim Kakangi ragamar Sashen Hausa. BBC ta naɗa shi editan sashen na tsawon shekara guda, bayan ya samu nasara a zagayen zaɓen da aka gudanar.

Sabon Shugaban sashen BBC hausa bahaushe

Kakangi ba sabon mutum ba ne a BBC. Ya kasance Babban Jami’in Kula da Labaran Intanet, kuma yana da gogewa sama da shekaru 10 a aikin jarida da samar da abubuwan da suka dace da kafafen dijital.

Nadinsa ya zo ne a lokacin da aikin jarida ke fuskantar sabon sauyi, inda kafafen sada zumunta, da bidiyo, da wayoyin hannu da basirar wucin gadi wato AI ke sauya yadda ake samarwa da kuma amfani da labarai.

Daga rediyo zuwa digital

Tarihin waɗannan shugabanni shida yana ba da wani hoto na yadda BBC Hausa kanta ta sauya cikin shekaru.

Daga zamanin da rediyo shi ne babban hanyar isar da sako, zuwa lokacin intanet, wayar hannu, talabijin, kafofin sada zumunta da kuma yanzu zamanin basirar wucin gadi wato AI.

Kowanne daga cikin shugabannin ya jagoranci sashen a wani lokaci daban na wannan tafiya.

Wasu sun mayar da hankali kan inganta aikin rediyo, wasu suka fuskanci zuwan intanet da wayoyin hannu, yayin da waɗanda suka zo daga baya suka shiga lokacin da digital ya zama ginshiƙin aikin kafar yaɗa labarai.

Yanzu tambayar da ke gaban sabon edita, Haruna Kakangi, ita ce: ina zai kai BBC Hausa a wannan sabon zamani na digital da AI?

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *