Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce jami’anta sun dakile wani harin ‘yan bindiga tare da kwato tumaki 43 da aka sace daga hannun maharan a ƙaramar hukumar Binji ta jihar.

Lamarin ya faru ne a daren ranar 30 ga Yuli, 2026, bayan samun kiran gaggawa cewa wasu ‘yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Anada, inda suka yi harbe-harbe tare da kwashe dabbobin al’umma.

Bayan samun rahoton, jami’an rundunar ‘yan sanda ta Binji tare da tawagar yaki da garkuwa da mutane sun gaggauta zuwa wurin, inda suka tare hanyoyin da ake zargin maharan za su bi.

Rundunar ta bayyana cewa jami’an sun yi arangama da ‘yan bindigar, lamarin da ya tilasta musu gudu zuwa cikin daji tare da barin dabbobin da suka sace.

An samu nasarar kwato dukkan tumaki 43 ba tare da an samu asarar rai ko jikkata ba.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto, CP Hayatu Hassan Shaffa, ya da jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimaka mata wajen dakile ayyukan masu aikata laifuka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *