Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT) ta ce ta kwato kayayyakin more rayuwa da aka lalata ko aka sace a sassa daban-daban na Abuja, tare da kama mutane biyar da ake zargi da hannu a aikata laifin
Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar rundunar.
Ya ce kayayyakin da aka kwato sun haɗa da murfunan magudanan ruwa da fitilun hasken rana na kan tituna da manyan igiyoyin lantarki da kuma igiyoyin sadarwar intanet, waɗanda satar su ke haddasa asarar dukiya da kuma jefa rayukan al’umma cikin haɗari
- Wike ya sha alwashin kammala duk ayyukan Titunan Abuja kafin ƙarshen 2026
- Tinubu ya rusa Kwamitin sa ido kan sayar da kadarorin gwamnati
- Yakin neman zabe na nuna abin da aka yi ne—Wike
A cewarsa, satar irin waɗannan kayayyaki na haifar da hadura a kan hanyoyi da jikkatar masu tafiya a ƙafa da ƙaruwar aikata laifuka a wuraren da suka shiga duhu, da kuma katse wutar lantarki ga al’ummomi da dama.
Sanusi ya ce an kwato kayayyakin ne a yayin samame da aka gudanar a yankunan Maitama da Garki da Durumi da Jabi da Apo Legislative Quarters da Lugbe da Nyanya.
Mutanen da aka kama sun haɗa da Godwin Aja da Mustapha Nasiru da Ibrahim Garba da Abdulrasheed Sale da Dabarani Mujitafa.
Hakazalika, Rundunar ta sanar da kwato lambobin motocin gwamnati da na diflomasiyya da wasu mutane ke amfani da su ba tare da izini ba.
Sanusi ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya gano cewa ana amfani da irin waɗannan lambobin wajen ɓoye masu aikata laifuka da kauce wa ganowa ko kamawa.
Ya bayyana cewa binciken ya gano masu amfani da lambobin ba bisa ƙa’ida ba, da kuma masu ƙera su da hanyoyin da ake samar da su.
A cewarsa, mutanen da aka kama suna tsare a hannun ’yan sanda, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala binci.
Kwamishinan ya tabbatar wa mazauna Abuja cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin rage aikata laifuka da tabbatar da tsaro a Babban Birnin Tarayya.