Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga Masarautar Saudiyya da ta haɗa gwiwa da Najeriya wajen faɗaɗa damar samun ilimin boko ga almajirai da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta, tana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da makomar ƙasar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Uwargidan Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai, Busola Kukoyi, ta fitar a ranar Alhamis, bayan ganawar da Oluremi Tinubu ta yi da Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
- Mu muka amince da Hukumar bogi ba tare da bin ka’idar da aka shimfida ba–Shugabar Ma’aikatan Tarayya
- Komai daidai ne a siyasa—Shugaba Tinubu: Martanin ‘yan Adawa
- Jihar Bauchi ta sami tallafin miliyoyin daloli daga Bankin ECOWAS (EBID)
Da take jawabi yayin ganawar, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta ce haɗa ilimin addinin Musulunci da ilimin boko zai samar wa almajirai damar samun ingantacciyar rayuwa, tare da taimakawa wajen magance wasu daga cikin matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta na dogon lokaci.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma yi kira da a samar da haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Saudiyya domin sake fasalin tsarin ilimin almajirai, inda ta jaddada cewa wannan haɗin gwiwar zai haɗa ilimin Larabci da na boko.
Remi ta kuma yaba da kyakkyawar alaƙar diflomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu, tare da gode wa jakadan Saudiyya bisa ziyarar da ya kai mata.
A nasa jawabin, Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, ya ce ya gamsu da irin kyakkyawar tarbar da aka yi masa tun bayan isowarsa Najeriya watanni biyar da suka gabata.
Ya bayyana cewa ya riga ya gana da mambobin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC), yana mai bayyana fatan cewa waɗannan tattaunawa za su ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki.
Ƙididdga daga hukumar kula da Almajirai da yaran da basa zuwa makaranta ta Najeriya na nuna cewa akwai kimanin yara miliyan 10.7 da basa zuwa makaranta a fadin Ƙasar.