Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Joseph Tegbe

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na dakatar da biyan tallafin wutar lantarki daga shekara ta 2027, domin magance abin da ta ce ƙaruwar bashin da ke kan ɓangaren wutar lantarkin.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan a wani taron tattaunawa da manema labarai.

Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya za ta fara rage biyan tallafin a hankali tun daga 2027, tare da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan sabuwar tsari ba za ta hana ‘yan ƙasa amfana da dimbin fa’idodin da suke samu a yanzu ƙarƙashin tsarin tallafin ba.

Tegbe ya ƙara da cewa duk da shirin dakatar da tallafin, babu wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a yanzu, inda ya jaddada cewa gwamnati ba ta tunanin ƙara ƙudin nan kusa, ya na mai cewa, “Za mu fara rage biyan tallafin wutar lantarki daga 2027. Duk da haka, babu wani shiri na ƙara kuɗin wutar lantarki a yanzu. Burinmu shi ne mu gina ɓangaren wutar lantarki da zai tsaya da ƙafafun sa ta fuskar kasuwanci, tare da kare masu rauni daga cikin masu amfani da lantarkin.”

Ya kara da cewa: “Asusun Taimakawa Masu Amfani da Wutar Lantarki zai taka muhimmiyar rawa wajen rage tasirin janye tallafin ga masu rauni yayin da muke aiwatar da waɗannan gyare-gyare,” in ji Ministan.

Har wa yau, Ministan ya jaddada cewa tallafin wutar lantarki na Najeriya ya dade yana zama nauyi mai yawa ga asusun gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *