Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya bada umurnin sakin dukkan kudaden da aka amince da warewa hukumomin raya yankuna.
Akume ya bayyana haka ne ranar Litinin, a taron koli na Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya, NCDC, mai taken “Babban cigaba: Tsarin shekaru 20 na raya tattalin arziki, ababen more rayuwa da cigaban Al’umma a yankin Arewa ta Tsakiya.”
Akume, wanda ya wakilci shugaban kasa a wajen taron, ya ce kafa hukumomin raya yankuna na daga cikin manufofin shirin (Renewed Hope Agenda) na gwamnatin Tinubu, da nufin gaggauta bunkasa yankuna daban-daban na kasar.
- Najeriya ta nemi sake fasalin tsarin shugabancin duniya a taron BRICS
- Rikicin Hormuz: Farashin litar man fetur ya kai 1,430 a Abuja
- Tinubu ya isa Paris don ci gaba da hutun shekara a Turai
Ya ce, gwamnati za ta ci gaba da bai wa hukumar NCDC da sauran hukumomin raya yankuna cikakken goyon baya, domin aiwatar da manyan ayyukan da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da masana’antu a Najeriya.
Sai dai shugaban kasar, ya ce hukumomin ba za su dogara kacokan kan kudaden gwamnati ba, inda ya bukace su da su nemi hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu, tallafin kungiyoyin bayar da agaji da kuma hanyoyin samun kudaden raya kasa domin aiwatar da manyan ayyukan da zasu kawo sauyi.
Ana sa ran hukumomin za su mayar da hankali kan manyan ayyuka da suka shafi layin dogo, sufurin jiragen sama, bunkasar masana’antu, tsaro, zuba jari, gina al’umma, ilimi da lafiya.
Akume, ya ce yankin na da kwarewa a fannin noma, hakar ma’adanai da samar da bunkasar masana’antu, yana mai jaddada bukatar sauya salo daga fitar da albarkatun kasa kai tsaye zuwa sarrafa su da kara musu daraja kafin sayar da su.