Masu aikin ceto a Indonesia, sun ci gaba da neman sama da mutane 100 da suka bace bayan wani jirgin ruwa mai dauke da fasinjoji ya kife a cikin tekun Java.
An tura jiragen soji, masu nutsewa karkashin ruwa domin gudanar da aikin neman wadanda suka tsira, kamar yadda shugaban hukumar kula da ayyukan ceto ta kasar, Mohammad Syafii, ya bayyana.
- China ta gabatar da tsare-tsare biyar don ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen BRICS
- Gobara ta jikkata mutane shida a wata masana’antar kayan wasanni a Indiya
- Mutane biyu sun jikkata a harin Houthi kan yankin Jazan na Saudiyya
Jirgin ruwan kamfanin yawon bude ido na Virgo Transport 8, wanda hukumomi suka ce yana dauke da fasinjoji 213 da ma’aikata 30, ya daina jin duriyar tashar Surabaya tun da sanyin safiyar Lahadi, birni na biyu mafi girma, da ke gabashin tsibirin Java a Indonesia.
Shugaban hukumar agajin gaggawa ta kasa, Mohammad Syafii, ya ce zuwa ranar Litinin, an tabbatar da mutuwar mutane shida, yayin da ake cigaba laluben wasu 129.
Syafii ya bayyana cewa an tura jiragen sama biyar da jiragen ruwa 17, ciki har da jiragen sojin ruwan kasar, domin taimakawa wajen aikin neman wadanda suka bace.
Hadurran jiragen ruwa dai na yawan faruwa a Indonesia, kasar da ke da tsibirai sama da 17,000, kuma take dogaro da zirga-zirgar jiragen ruwa wajen harkokin yau da kullum da kuma yawon bude ido.