Gobara ta tashi a wata masana’antar kera kayan wasan judo da safar hannu na dambe a yankin Swaroop Nagar da ke birnin Delhi na Indiya, inda mutane shida suka jikkata.

‘Yan sanda sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na ANI cewa, tashin gobarar ya haifar da firgici, lamarin da ya sa wasu mazauna wani gini da ke fuskantar masana’antar tsalle daga gidajensu domin tsira.

Gobarar ta tashi ne a bene na ƙasa da bene na farko na wani gini da ke Khasra mai lamba 357/58, a Gali ta biyu dake Swaroop Nagar.

Rahotanni sun ce an sanar da ofishin ‘yan sandan Swaroop Nagar game da lamarin.

Sai dai, babu wani mutum da gobarar ta jikkata kai tsaye.

An tura motocin kashe gobara zuwa wurin, inda jami’an kashe gobarar suka yi nasarar shawo kan wutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *