Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya isa birnin Paris na ƙasar Faransa domin ci gaba da hutun shekara na tsawon makonni uku da yake yi a Turai, kamar yadda jami’an da ke kusa da shugaban suka shaida wa jaridar The PUNCH a ranar Lahadi.

Jakadan Najeriya a Faransa, Ayodele Oke, ne ya tarbi shugaban bayan isarsa Paris, kamar yadda hotunan da aka bai wa The PUNCH suka nuna.

Tinubu ya bar Abuja a ranar Lahadi, 30 ga Agustan 2026, domin fara hutun makonni uku, inda London ta kasance zangon farko kafin ya wuce Paris domin ci gaba da hutun.

Paris na daga cikin biranen ƙasashen waje da Shugaba Tinubu ya fi yawan ziyarta.

Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Tinubu ya ziyarci Paris aƙalla sau 13, inda ya shafe sama da kwanaki 50 a birnin a yayin ziyarce-ziyarcen aiki na gwamnati da kuma na kashin kansa.

Ficewar shugaban daga Najeriya ta zo ne mako guda bayan fitar da jerin sunayen Kwamitin Yakin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, wanda ya sanya Tinubu a matsayin shugaban kwamitin, yayin da mataimakinsa, Kashim Shettima, aka nada shi mataimakin shugaban kwamitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *