‘Yan bindiga sun kashe makiyaya uku da shanu kusan 50 a yankin Aloghom na Ƙaramar Hukumar Mangu, a Jihar Filato.
Sabon harin ya faru ne kwana ɗaya bayan da aka ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kashe wani makiyayi mai suna Yakubu Ishaku a yankin Nyerwe na Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi na jihar.
Hashimu Yahaya, Ko’odinatan Ƙungiyar Fulani ta (Fulbe Fulani Development Association) ta Ƙaramar Hukumar Mangu, ya bayyana harin a matsayin rashin imani, inda ya ce an kashe wadanda abin ya shafa ne yayin da suke gudanar da ayyukansu.
-
BRICS ta ce Bankin NDB zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa
-
Dakatar da yaki: Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun goyi bayan BRICS
-
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Bamanga Tukur, ya rasu.
Ya bayyana sunayen waɗanda aka kashe da Garzali Shaibu, mai shekara 18; Bashiru Yakubu, mai shekara 14; da Salim Abubakar, mai shekara 15.
Haka kuma, Shugaban Ƙungiyar (Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria) MACBAN, na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce ‘yan bindigar sun mamaye wurin kiwon sannan suka buɗe wuta yayin da wadanda abin ya shafa suke kula da shanunsu.
Ya ce: “Makiyayan na kula da shanunsu ne kawai sai suka ga maharan suka kai musu hari, suka fara harbi kan mai uwa da wabi. A ranar Alhamis, sun kashe makiyayi ɗaya da shanu 18 a Nyerwe. A yau kuma, sun kashe makiyaya 3 da shanu 50.
“Wannan hari ne mara tushe domin makiyayan na gudanar da ayyukansu cikin lumana. Hakan ya nuna a fili ƙarara cewa wannan wani shiri ne don kawar da fulani makiyaya a Filato. Mun sanar da dukkan hukumomin tsaro da suka dace a jihar, ciki har da Hukumar DSS da Operation Enduring Peace,” in ji shugaban na jihar.
Babayo ya ƙara yin Allah-wadai da harin, inda ya buƙaci makiyaya a jihar da su ci gaba da kwantar da hankula da kuma kasancewa masu biyayya ga doka da oda.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Operation Safe Haven, Kyaftin Polycarp Oteh, bai amsa tambayoyin da ‘yan jarida suka yi masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
