Ƙasashen BRICS sun bayyana a ranar Asabar cewa Bankin bunkasa tattalin arzikin kasashen BRICS (NDB) zai kasance muhimmiyar cibiya wajen inganta ci gaba mai ɗorewa, rage rashin daidaito da kuma ƙarfafa ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa.
Ƙasashen BRICS sun kuma ƙarfafa bankin da ya ci gaba da faɗaɗa ƙarfinsa wajen tattara kuɗaɗe, inganta kirkire-kirkire, ƙara ba da rancen kuɗi cikin kuɗaɗen ƙasashe, da kuma faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansa.
Sun ce hakan zai taimaka wajen tallafa wa manyan ayyuka da ke inganta ci gaba mai ɗorewa, rage rashin daidaito, bunƙasa zuba jari a ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa haɗin kan tattalin arzikin ƙasashe.
- Shugabannin BRICS sun nuna damuwa kan harajin bai ɗaya na WTO
- ƙungiyar BRICS ta amince da yarjejeniyar New Delhi
- Taron Kungiyar BRICS: Abubuwan da za a tattauna da muhimmancin su
Ƙasashen sun kuma bukaci NDB ya ci gaba da bin tsarin da ƙasashe mambobi ke jagoranta da kuma aiwatar da ayyuka bisa buƙatun mambobi, tare da ƙara ƙarfafa tsarin shugabancinsa domin inganta juriyar cibiyar da kuma ingancin ayyukanta.
Haka kuma, BRICS ta sake jaddada goyon bayanta ga ƙara yawan ƙasashen da ke cikin mambobin NDB, tare da yin kira da a gaggauta duba buƙatun ƙasashen BRICS masu sha’awar shiga bankin, bisa tanadin dabarun bankin da manufofinsa.
Ƙasashen BRICS ne suka kafa Bankin bunkasa tattalin arzikin (NDB) a shekarar 2015 domin tallafa wa ayyukan ci gaba da zuba jari a ƙasashe masu tasowa.