Firaministan Indiya, Narendra Modi, na karbar bakuncin taron shekara-shekara na kungiyar BRICS, wanda ya fara yau Asabar a birnin New Delhi, babban birnin kasar.
An kawata birnin da allunan talla masu taken BRICS, yayin da aka haskaka gine-gine da wuraren zagayawar ababen hawa domin taron.
Fiye da shugabannin kasashe 12 ne ke halartar taron na 18 na kungiyar, wadda ake kallon wata kungiya da za ta iya kalubalantar kawancen tattalin arziki da kasashen Yammacin duniya masu arziki suka mamaye.
A shirye-shiryen taron, an kara tura jami’an tsaro kusan 30,000, yayin da aka rufe wasu tituna da ke kusa da otal-otal din da shugabannin kasashen suka sauka.
Shugabanni da suka hada da Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Iran Masoud Pezeshkian da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, sun isa New Delhi ranar Juma’a domin gudanar da ganawar bangarori biyu da Firaministan Indiya Narendra Modi.
Shugaban China Xi Jinping, wanda ke ziyartar Indiya a karon farko cikin shekaru bakwai, ya isa kasar a safiyar yau Asabar.
Ana sa ran Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, wanda zai halarci taron, zai tattauna batun yakin.
Wannan shi ne karon farko da ya ziyarci Indiya tun bayan zama shugaban Iran, sannan kuma shi ne karon farko cikin shekaru takwas da shugaban Iran ya ziyarci yankin kudancin Asiya.
Taron na kwanaki biyu, wanda za a gudanar a ranakun 12 da 13 ga watan Satumba, na gudana ne a daidai lokacin da duniya ke fuskantar rikice-rikice da dama, ciki har da yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran, yakin Rasha da Ukraine, da kuma rikice-rikicen kasuwannin makamashi na duniya.
- Trump ya zargi Iran da kai hari kan bututun mai na Saudi Arabiya
- Bore yayi ajalin mutane 7 a wani gidan yari a arewacin Siriya
- Saudiyya ta rufe bututun mai na East-West bayan hare-hare
Sai dai kungiyar BRICS na fuskantar kalubale daga cikin gida, yayin da ake samun sabanin ra’ayi tsakanin mambobinta kan yakin Amurka da Isra’ila da Iran, ci gaba da rikicin Saudiyya da kungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran a Yemen, da kuma takaddamar iyaka tsakanin Indiya da China.
Babban manufar BRICS ita ce mambobin kungiyar su rage tasirin da cibiyoyin kasa da kasa karkashin jagorancin kasashen Yammacin duniya ke da shi, musamman a fannin tattalin arziki.
A bana, yayin da Indiya ke jagorantar kungiyar, taken taron shi ne “Gina Juriya da Kirkire-kirkire da Hadin Gwiwa da Dorewa.”
Taron na bana zai mayar da hankali kan ƙarfafa tattalin arzikin kasashen mambobin kungiyar ta hanyar cinikayya da hadin gwiwa a fannin makamashi da musayar ilimi kan fasahar AI da sauran fasahohi.
Alicia García-Herrero, babbar masaniyar tattalin arziki ta yankin Asiya da Pacific a kamfanin hada-hadar kudi na Faransa Natixis, ta ce shugabannin za su kuma tattauna hanyoyin biyan kudaden cinikayya tsakanin kasashe, musamman a yayin da kasashen Yammacin duniya suka kakaba wa wasu mambobin BRICS, ciki har da Rasha, takunkumi.
Ta ce hakan ba yana nufin kungiyar za ta yi kokarin maye gurbin dalar Amurka ba.
Kremlin ta bayyana ranar Alhamis cewa Rasha za ta tattauna da sauran kasashen abokan hulda na BRICS kan amfani da kudaden dijital wajen biyan kudaden cinikayya a yayin taron da ake yi a New Delhi.
Wani masani kan dabarun siyasa, Manoj Kewalramani, ya ce wadannan batutuwa na daga cikin muhimman abubuwan da shugabannin BRICS za su tattauna domin tabbatar da tsaron hanyoyin samar da kayayyaki da kuma rage illolin rikice-rikicen da ake fama da su a duniya.
Taron na bana na zuwa ne sama da watanni shida bayan fara yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran.
A watan Mayu, taron ministocin harkokin wajen BRICS ya kasa fitar da matsaya ta bai daya wajen yin Allah-wadai da yakin da ake yi da Iran.
Ana sa ran Shugaban Iran Masoud Pezeshkian, wanda zai halarci taron, zai tattauna batun yakin.
Wannan shi ne karon farko da ya ziyarci Indiya tun bayan zama shugaban Iran, sannan kuma shi ne karon farko cikin shekaru takwas da shugaban Iran ya ziyarci yankin kudancin Asiya.
Masanin harkokin siyasa a Jami’ar Hong Kong, Alejandro Reyes, ya ce kasancewar Iran mamba a BRICS da kuma yadda rikicin ke shafar hanyoyin cinikayya da samar da makamashi na da matukar tasiri ga tattalin arzikin duniya.
Sai dai ya ce rikicin da ke tsakanin Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ita ma mamba ce a BRICS, dangane da yakin, na iya sanya samun matsaya daya tsakanin kasashen kungiyar kan lamarin ya zama mai wahala.
Tun bayan fara yakin Amurka da Isra’ila da Iran, Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan kadarorin sojin Amurka da ababen more rayuwar fararen hula a kasashen yankin Gulf, ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ya zuwa yanzu, hare-haren Iran sun kashe mutane 15 a UAE, ciki har da jami’an soji biyu, wani ma’aikacin farar hula da ke aiki da sojoji, da wasu fararen hula 12.
Haka kuma, UAE ta sanar da dakatar da cinikayya da Iran ba tare da kayyade lokacin da za a kawo karshen matakin ba a watan Agusta.