Wani boren fursunoni ya haddasa gobara a wani gidan yari da ke garin Kobani, mai yawan Kurdawa a arewacin Siriya, inda rahotanni suka ce akalla mutane bakwai sun mutu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Siriya SANA ya ruwaito cewa gobarar ta tashi ne bayan fursunoni sun yi bore, sakamakon rikicin da ya barke a garin tsakanin Kurdawa da Larabawa.

Har yanzu mayakan Kurdawa ne ke kula da gidan yarin, duk da cewa dakarun gwamnatin Siriya sun shiga garin da ke kan iyakar kasar da Turkiyya a baya-bayan nan.

Kungiyar sa ido kan hakkin dan Adam ta Siriya, da ke da hedikwata a Birtaniya, ta ce boren ya samo asali ne daga shirin hukumomi na mayar da wasu fursunoni zuwa wani gidan yari da ke birnin Aleppo.

Kobani, wanda kungiyar IS ta kewaye kimanin shekaru goma da suka gabata, ya kasance cibiyar da aka fara kai hare-haren mayakan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka, wadanda suka fatattaki ‘yan tsagerun kungiyar daga yankin karshe da suke rike da shi a shekarar 2019.

A ranar Juma’a ne kuma aka samu wani bore a Kobani, bayan da Kurdawa suka zargi Larabawa da kashe wani mutum bakurde.

Rikici tsakanin tsirarun Kurdawa da gwamnatin tsakiya ta Siriya na ci gaba da kasancewa mai tsanani, duk da matakan baya-bayan nan na mayar da arewa maso gabashin kasar karkashin ikon sabuwar gwamnatin da ke Damascus.

A karshen watan Agusta, kwamandan Rundunar Demokradiyyar Siriya (SDF) mai rinjayen Kurdawa, wadda ke samun goyon bayan Amurka, ya sanar da rushe rundunar a hukumance.

Rundunar dai a baya tana iko da wani yanki mai cin gashin kansa a arewa maso gabashin Siriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *