Najeriya ta yi kira da a gaggauta sake fasalin tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe na ƙasa da ƙasa, domin samar da tsarin da zai fi dacewa da sauye-sauyen tattalin arziki da alƙaluman jama’a na duniya a halin yanzu.
Wannan na ƙunshe ne cikin jawabin da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gabatar a madadin Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a yayin taron ƙasashen BRICS na shekarar 2026.
A cikin jawabin, Shettima ya nemi samar da tsarin shugabanci na duniya da zai kasance mai wakilci da adalci da kuma mai saurin amsa buƙatun ƙasashe daban-daban.
- China ta gabatar da tsare-tsare biyar don ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen BRICS
- Tinubu ya isa Paris don ci gaba da hutun shekara a Turai
- Kashim Shettima ya jaddada aniyar Nijeriya ta gudanar da aiki da WTO
Shettima kuma jaddada goyon bayan Najeriya ga cibiyoyin duniya da ke nuna ainihin yanayin tattalin arziki da yawan al’ummar duniya a wannan zamani.
A cewar sa, ƙungiyar BRICS na ƙara ƙarfafa muryar ƙasashen Global South, tare da taimakawa wajen samar da tsarin duniya mai yalwar dama da wakilci.
Wannan matsaya ta Najeriya ta yi daidai da kiranta na ganin an sake fasalin cibiyoyin duniya domin su yi daidai da sauye-sauyen tattalin arziki da alƙaluman jama’a na zamani.
Haka kuma, Najeriya ta gayyaci masu zuba jari na ƙasashen waje da su yi amfani da damar zuba jari da ke akwai a ƙasar, tare da kallon Najeriya a matsayin wata ƙofar zuwa babbar kasuwar Afirka da ke ci gaba da bunƙasa ƙarƙashin Yarjejeniyar Ciniki cikin ’Yanci ta Nahiyar Afirka (AfCFTA).