Najeriya ta bayyana burinta na karɓar baƙuncin Gasar Motsa Jiki ta ‘yan ƙasa da shekaru 20 ta 2030, yayin wani muhimmin taro tsakanin Babban Darakta na Hukumar Wasanni ta Ƙasa, NSC, Bukola Olopade, da jami’an shirya gasar ta duniya a Budapest, dake ƙasar Hungary.

Taron wanda aka gudanar a lokacin buɗe Gasar (World Athletics Ultimate Championships), ya mayar da hankali kan buƙatar Najeriya na karɓar baƙuncin gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta matasa a shekarar 2030.

Olopade ya tabbatar wa hukumar shirya gasar cewa Najeriya ta himmatu wajen samar da ababen da ake buƙata na shirya gasar, da bin ƙa’idojin gudanarwa da kuma karramawar da ake buƙata domin gudanar da gasar ta ƙasa da ƙasa.

Babban Daraktan na NSC ya bayyana samun ƙaruwar masu saka jari a fannin samar da ababen more rayuwa na ‘yan wasanni, da habɓaka ‘yan wasa da kuma gudanar da gasa.

Hakan na zuwa ne sakamakon nasarar da Najeriya ta samu kwanan nan wajen gudanar da manyan gasa na wasannin guje-guje da tsalle-tsalle.

A watan Yulin 2025, Najeriya ta karɓi baƙuncin Gasar Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Matasa ’yan kasa da shekaru 18 ta nahiyar Afirka (CAA Africa) a Abeokuta, Jihar Ogun, inda gasar ta samu halartar ƙasashen Afirka fiye da 40 da kuma ‘yan wasa kusan 1,000, da jami’ai da sauran mahalarta.

Nasarar gudanar da gasar ta nahiyar ta nuna cewa Najeriya na da ƙarfin shirya manyan gasa na wasannin guje-guje da tsalle-tsall.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *