Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce Iran, na ƙoƙarin “kawar da shi” daga kan mulki saboda a cewar sa, Tehran na ganin cewa jam’iyyar Democrat za ta bari ta mallaki makamin nukiliya ba.

Ba za su mallaki makamin nukiliya ba

Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Ya ce manufar sa, ta amfani da jiragen yaƙi samfurin B-2 wajen kai hare-hare, ke hana Iran samun damar kera ko mallakar makamin nukiliya.

A cewar shugaban na Amurka, Iran na ganin cewa idan har ya bar mulki, musamman idan jam’iyyar Democrat ta sake samun iko a Washington, za a sassauta mata matsaya kan shirinta na nukiliya.

“Ba za su mallaki makamin nukiliya ba,” Trump ya jaddada, yana mai cewa hakan na daga cikin manyan dalilan da suka sa Amurka ta shiga yaƙi da Iran.

Trump, ya nanata cewar ba ya nadamar matakin soji da ya ɗauka kan Iran, kuma idan aka sake ba shi damar yanke shawara, zai sake yin abin da ya yi.

Ya ce hare-haren da Amurka ta kai sun lalata ƙarfin nukiliyar Iran, duk da cewa batun irin barnar da aka yi da kuma ko an kawar da dukkanin abubuwan da Iran ke da su na nukiliya ya ci gaba da kasancewa abin muhawara.

A halin da ake ciki, batun shirye-shiryen nukiliyar Iran na ci gaba da kasancewa babban abin da ke haddasa takaddama tsakanin Tehran da Washington.

Haka kuma, rikicin ya ƙara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rashin tabbas, musamman makomar Mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen safarar man fetur daga yankin zuwa sauran sassan duniya.

A baya-bayan nan, Amurka da Iran sun yi musayar wuta kan mashigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *