Ƙasar Jordan na taka muhimmiyar rawa a tsaron Gabas ta Tsakiya, kasancewar ta babbar ƙawar Amurka, da ke baiwa sojojin ta damar amfani da wasu sansanonin soja da ke cikin ƙasar ta.
Matsayin Jordan, yana ƙara fitowa da muhimmancin ta yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ƙara tsananta, inda sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar suka zama wani muhimmin ɓangare na ayyukan sojin Washington a yankin.
Daga cikin sansanonin akwai Muwaffaq Salti Air Base, wanda ke daga cikin wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su wajen gudanar da kaiwa hare-hare a Gabas ta Tsakiya.
A wani sabon hari da Iran ta kai sansanin, rahotanni sun ce wasu jiragen yaƙin Amurka sun lalace, ciki har da wani jirgin yaki samfurin (A-10 Thunderbolt), da ya rasa ɗaya daga cikin fikafikansa, yayin da wasu jiragen F-15 guda takwas suma suka tarwatse.
Jordan, na taka rawa wajen kare sararin samaniyar ta, inda sojojin ta ke ƙoƙarin dakile makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi da ake harbowa daga Iran da wasu kasashen yankin.
Ƙasar, na da girman matsayi a taswirar Gabas ta Tsakiya, kasancewar ta makwabciyar da Isra’ila, Syria, Iraq da Saudi Arebiya, wannan ya sanya take da matuƙar muhimmanci wajen tsaron yankin.
Duk da cewa Jordan, ba ta cikin yaƙin Amurka da Iran kai tsaye, kasancewar sojojin Amurka a ƙasar na sanya ta cikin ƙasashen da rikicin ka iya shafa, musamman idan hare-haren Iran suka nufi sansanonin Amurka da ke yankunan ta.