Hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta ce za ta ƙara ƙarfafa matakan tsaro da kare lafiyar ma’aikata, ’yan bautar ƙasa, baƙi da kadarorin gwamnati a dukkan ofisoshinta.

Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron horas da jami’an kula da lafiya, tsaro da muhalli na hukumar karo na farko a Abuja.

Nafiu, wanda Daraktan kula da albarkatun ɗan’adam, Nura Umar, ya wakilta, ya ce hukumar za ta riƙa gano haɗurran wurin aiki, tantance haɗari da ɗaukar matakan hana raunuka da cututtuka.

Ya buƙaci ofisoshin NYSC su riƙa duba wuraren aiki, kula da kayan kariya, gudanar da atisayen kashe gobara da kuma tanadin kayan agajin gaggawa.

Ya ce ya kamata a riƙa yin rigakafin haɗari maimakon jira sai an samu matsala.

Daraktar sashen kula da ayyukan gama-gari, Yetunde Baderinwa, ta ce taron zai taimaka wajen samar da tsari mai ɗorewa na kare lafiya da muhalli a ofisoshin NYSC.

Mahalarta taron sun haɗa da jami’an kula da lafiya, tsaro da muhalli daga sakatariyoyin jihohi 36 da Abuja.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *