Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya takwaransa na Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, murnar sake zaɓensa a matsayin shugaban ƙasar, yana mai fatan sabon wa’adinsa zai ƙara ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar ranar 26 ga Oktoba, 2026, Tinubu ya ce sake zaɓen Lula ya ba ƙasashen biyu damar bunƙasa dangantakar tarihi da abota da ke tsakaninsu.
- Uzodimma ya bukaci ’yan jarida su fifita gaskiya da riƙon amana
- WHO ta ce babu sauran mai cutar Ebola a Najeriya
Tinubu ya ce Najeriya da Brazil, a matsayinsu na manyan ƙasashen Kudancin Duniya, za su iya ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da kare muradunsu a tsarin duniya mai sauyawa.
Ya bayyana cewa Najeriya na son faɗaɗa haɗin gwiwa da Brazil a fannonin kasuwanci da zuba jari, noma da samar da abinci, makamashi, masana’antu, kimiyya da fasaha, ilimi, sufurin jiragen sama da musayar al’adu.
Tinubu ya tabbatar da aniyar Najeriya ta ci gaba da aiki tare da Brazil wajen ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe da cimma muradun bai ɗaya a Afirka, Kudancin Amurka da sauran ƙasashen Kudancin Duniya, tare da yi wa Lula fatan samun nasara a sabon wa’adinsa.