Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya jaddada cewa kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da riƙon amana da bunƙasa dimokuraɗiyya a Najeriya.
Uzodimma ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lacca mai taken “Media, Democratic Consolidation and Development” a lacca ta uku ta tunawa da Raymond Aleogho Dokpesi kan sadarwa da ci gaba.
- Sojoji sun bayyana dalilin arangamarsu da ’yan sanda a Filato
- Peter Obi ya yi Allah-wadai da cin zarafin magoya bayansa
Ya ce bai kamata a riƙa kiyaye ƙa’idojin dimokuraɗiyya a lokacin zaɓe kawai ba, domin ya kamata shugabanni, hukumomi da ’yan ƙasa su riƙa mutunta su a kowane lokaci.
Gwamnan ya buƙaci ’yan jarida su riƙa dogaro da sahihan bayanai da ƙididdiga, tare da kiyaye ƙa’idojin ƙwarewa da ɗaukar nauyin da ke kansu wajen yaɗa labarai.
Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ce ta shirya laccar domin tunawa da marigayi Raymond Aleogho Dokpesi, tare da inganta ƙwarewa, kishin ƙasa da riƙon amana a aikin jarida.