Dakarun Operation Tabbatar da Zaman Lafiya sun ce sun tura jami’ansu yankin Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato ne bayan samun kiran neman ɗaukin gaggawa kan harbe-harbe da kuma kisan wani mazaunin yankin, Adamu Suleiman, a ranar 20 ga Oktoba, 2026.

 

A sanarwar da jami’in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, ya fitar ranar 25 ga Oktoba, rundunar ta ce harbe-harben ya shafi Mai Farin Moto, Maraban Dere da wasu yankunan da ke maƙwabtaka da su.

Sanarwar ta ce bayan isa yankin, sojojin sun yi ƙoƙarin tattaunawa da jami’an ’yan sanda da ke gudanar da aiki a wurin domin fahimtar halin da ake ciki da kuma daidaita matakan tsaro.

Sai dai rundunar ta ce wasu jami’an ’yan sandan ba su ba da haɗin kai ba, duk da ƙoƙarin da aka yi na kwantar da hankula.

Rundunar ta jaddada cewa tura sojojin ya biyo bayan kiran neman taimako ne, da nufin kare rayuka da dukiyoyi da kuma hana matsalar tsaro ta ta’azzara.

Ta ce ana duba abubuwan da suka faru ta hanyoyin umarnin rundunoni da haɗin gwiwar hukumomin tsaro domin gano gaskiyar lamarin da kuma hana sake faruwarsa.

Operation Tabbatar da Zaman Lafiya ta buƙaci jama’a da ’yan jarida su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, tare da guje wa rahotannin da ba a tabbatar da su ba.

Rundunar ta kuma tabbatar wa mazauna Filato cewa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da doka da oda, kare fararen hula da ƙarfafa zaman lafiya a yankin da take gudanar da ayyukkanta

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *