Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Faransa ta bayar da rahoton mutum na farko da aka sani ya kamu da cutar Shamonda, wadda aka fi sani da cutar da ke shafar dabbobi, a watan Oktoba na shekarar 2026.
Cutar ta fi shafar dabbobi kamar shanu, tumaki, awaki da dawakai.
An fara gano ƙwayar cutar a cikin shanu a Najeriya a shekarar 1965, kuma tun daga lokacin an gano ta a wasu ƙasashe.
’Yan jarida a Afirka sun yi gargaɗin kan illar AI ga ayyukan jarida
WHO ta ce cutar shan inna na iya sake yaɗuwa idan ba a kawar da ita gaba ɗaya ba
Ana zargin cutar Shamonda na yaɗuwa ta hanyar cizon ƙananan ƙwari masu kama da ƙudaje, waɗanda ke iya ɗaukar ƙwayar cutar daga dabba zuwa wata.
A shekarar 2026, an gano cutar a Turai a karon farko, ciki har da Jamus, Switzerland, Austria, Belgium da Faransa.
WHO ta ce kawo yanzu mutum ɗaya ne kawai aka samu rahoton kamuwarsa da cutar, don haka masana kimiyya ba su da cikakken bayani kan yadda cutar ke shafar mutane ko yadda take yaɗuwa a tsakanin su.
Hukumar ta bayyana cewa a halin yanzu babu takamaiman allurar rigakafi ko maganin cutar Shamonda, tana mai cewa ana buƙatar ƙarin bincike domin fahimtar tasirinta ga mutane da hanyoyin yaɗuwarta.
A cewar WHO, ana kuma buƙatar ƙarin bayanai kafin a fahimci haɗarin da cutar ke iya haifarwa ga lafiyar ɗan Adam.