Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci a saki Rilwan Olawale, tare da yin Allah-wadai da abin da ya kira tsoratarwa da cin zarafin magoya bayansa a faɗin ƙasar.
Obi ya zargi Shugaba Bola Tinubu da raunana dimokuraɗiyya ta hanyar ƙarfafa tashin hankali, yana mai cewa ya kamata a mutunta ’yancin ’yan Najeriya na goyon bayan ɗan takarar da suka zaɓa.
- EFCC ta kama Sinawa 14 da ɗan Najeriya a masana’antun sarrafa lithium ba bisa ƙa’ida ba
- Sojoji sun bayyana dalilin arangamarsu da ’yan sanda a Filato
Ya ce kamfen ɗinsa na siyasa yana gudana cikin lumana, bisa manufofin ƙwarewa, riƙon amana, adalci da tausayi, kuma ba za su bari a tsorata su har su yi shiru ba.
Obi ya buƙaci a bayyana gaskiya game da kama Olawale, a saki shi, tare da mutunta haƙƙoƙinsa da kuma kawo ƙarshen abin da ya kira cin zarafin da ake yi wa magoya bayansa saboda siyasa.
Ya jaddada cewa za su ci gaba da bin hanyar zaman lafiya, amma za su yi amfani da hanyoyin doka wajen kare haƙƙoƙinsu na dimokuraɗiyya.